Salehi: Iran Ba Za Ta Amince Da Wani Sharadi Kan Komawar Amurka Cikin Yarjejeniyar Nukiliya Ba

2020-12-22 15:03:35
Salehi: Iran Ba Za Ta Amince Da Wani Sharadi Kan Komawar Amurka Cikin Yarjejeniyar Nukiliya Ba

Shugaban hukumar makamshin nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salehi ya bayyana cewa, Iran din ba za ta amince da duk wani sharadi dangane da komawar Amurka cikin yarjejeniyar nukiliya ba.

A zantawarsa da wasu kafofin yada labarai a daren jiya, Shugaban hukumar makamshin nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salehi ya jaddada cewa, babu batun amincewa da duk wani sharadi da Amurka za ta iya gabatarwa domin dawowarta a cikin yarjejeniyar nukiliya da aka rattaba hannu a kanta tsakanita da manyan kasashen dun

Ya ce Amurka ita kadai ce ta fice daga cikin wannan yarjejeniya, saboda haka za ta iya dawowa a duk lokacin da ta ga damar yin hakan, amma kuma ba ta da hakkin kafa wasu sharudda kan komowarta.

Tun a cikin shekara ta 2015 ne aka cimma yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, amma shugaban Amurka Doald Trump ya fitar da kasarsa daga cikin yarjejeniyar a cikin shekara ta 2018, tare da dawo da takunkuman Amurka kan kasar ta Iran da nufin karya ta.

Sai dai a nasa bangaren zababben shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyarsa ta mayar da Amurka a cikin wannan yarjejeniya a lokacin yakin neman zabe, da kuma bayan lashe zaben Amurka.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!