Zimbabwe Ta Kaddamar Da Shirin Musayar Amfanin Gona

2020-12-22 14:56:43
Zimbabwe Ta Kaddamar Da Shirin Musayar Amfanin Gona

Gwamnatin Zimbabwe ta kaddamar da wani shiri na musayar amfanin gona, wanda zai baiwa manoma damar sayar da amfanin gonarsu bisa farashin da kasuwa ta kayyade.

A baya dai kasar tana da tsarin musayar amfanin gona, amma daga bisani aka rufe tsarin, lokacin da gwamnati ta baiwa hukumar kayyade farashin amfani gona ta kasar (GMB) iznin saye da sayar da masara da alkama a shekarar 2001.

Sai dai a jawabinsa yayin kaddamar da shirin, ministan kudin kasar Mthuli Ncube ya ce, za a taimakawa tsarin ta hanyar baiwa manoma takardar shaidar karbar amfanin gonan da suka kai runbun adana kayayyaki.

Hakan na nufin, gwamnati za ta tsame hannunta wajen sanya farashin amfanin gona.

Haka kuma tsarin musayar, zai samar da wata kasuwa ga manoma a fannonin musayar amfanin gona, wanda ya hada da kanana da manyan manoma, da masu saye, da masu sanya ido, da ‘yan sari, da bankuna da masu kula da manyan dakunan adana amfanin gona da sauransu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!