​Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kasafin Shekara ta 2021

2020-12-22 14:00:45
​Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kasafin Shekara ta 2021

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da kasafin kudi na 2021 wanda yawansa ya kai fiye da naira Tiriliyan N13.5.

Rahotanni sun an samu karin sama da naira biliyan 500 daga kasafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiko wa majalisar wanda ya kai naira tiriliyan N13.082,420,568,233 tun da farko.

Hakan kuma ya bada damar cike gibin wasu wuraren da hadakar kwamitocin majalisar wakilai da ta dattawa suka nemi shugaban kasa da ya yi hakan, domin tabbatar da gudanar da ayyukan da za su kai ga inganta rayuwar ‘yan kasa.

Amincewa da kasafin kudin ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan kasafi ya gabatar ne , inda shugaban kwamitin kasafi na majalisar, Sanata Jibrin Barau, ya mika rahoton nasu a gaban majalisar yayin zamanta na jiya Litinin.

Ita dai majalisar Dattawan ta cimma matsayar amincewa da kudin da ya kai tiriliyan N5,641,970,060,680 a matsayin kudin gudanar da ayyukan yau da kullum, Sannan kuma majalisar ta amince da tiriliyan N4,125,149,354,222 a matsayin kudin gudunmawar da za ta tattara domin gudanar da manyan ayyukan raya kasa, tare da kashe naira tiriliyan N3,324,380,000,000 na biyan bashi, duk a cikin kasafin na 2021.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!