​Laliga: Benzema Ya Lashe Kyautar Zakaran Kwallon Kafa Na Gasar Laliga Ta Spain 2020

2020-12-22 13:53:34
​Laliga: Benzema Ya Lashe Kyautar Zakaran Kwallon Kafa Na Gasar Laliga Ta Spain 2020

Dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa Karim Benzema da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ya lashe kyautar zakaran kwallon kafa na gasar Laliga ta Spain 2020.

Hukumar wasannin kwallon kafa ta kasar Spain ta sanar da cewa, ta zabi Karim Benzema a matsayin dan wasan da ya taka leda yadda ya kamata a shekara 2020 a gasar Laliga ta kasar Spain.

Shekaru 10 a jere dai ‘yan wasa biyu ne kawai suke daukar wannan kyauta, su ne Cristiabo Ronaldo tsohon dan wasan Real Madrid, da kuma Lionel Messi, dan wasan Barcelona, inda a shekarar bana Karim Benzema ya samu nasarar daukar wannan kyauta.

Karim Benzema wanda musulmi ne dan kasar Faransa, wanda asalinsa balarabe ne dan kasar Aljeriya, ya bayyana farin cikinsa matuka dangane da daukar wannan kyauta a shekarar ba.

Haka nan kuma hukumar wasanni ta kasar Spain ta zabi Zainuddin Zidane mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a matsayin mai horar da ‘yan wasa da ya fi nuna kwazo a cikin shekara ta 2020.

Kamar yadda kuma aka zabi Lionel Messi a matsayin dan wasan da yafi saka kwallaye a cikin wannan shekara a gasar ta Laliga.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!