Rasha Ta aike Da Sojoji A Afrika Ta Tsakiya

2020-12-22 09:50:14
Rasha Ta aike Da Sojoji A Afrika Ta Tsakiya

Rasha ta sanar da aikewa da sojoji zuwa jamhuriyar Afrika ta tsakiya, bayan yunkurin ‘yan tawayen kasar da ake dangantawa da neman yin juyin mulki gabanin babban zaben kasar na ranar Lahadi mai zuwa.

Ko da yake labarin bai ambato yawan sojojin ba, amma ya ce wannan bukata ce daga gwamnatin Afrika ta tsakiya, duba da zaman dar-dar da ake ciki game da barazanar gungun masu dauke da makamai.

Kafin hakan dama Rasha ta ce ta damu matuka game da halin da ake ciki a wannan kasa ta Jamhuriyar AFrika ta tsakiya data yi fama da yake yake.

Gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta tsakiyar dai na mai zargin tsohon shugaban kasar François Bozizé, da yunkurin yi ma ta juyin mulki, batun da yake ci gaba da musantawa.

A nata bangare dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin da ke neman tayar da rikici a kasar da su kai zuciya nesa a yayin da ake daf da tunkarar manyan zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar a ranar 27 ga watan nan.

Yanzu hakan dai an baza dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya cikin fadin kasar domin dakile duk wata fitina da ka iya kawo illa ga zaben kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!