Iran Da Kasashe 4 Da Suke Cikin Yarjejeniyar Nukiliya, Sun Amince Da Aiwatar Da Ita Kamar Yadda Ya Dace
2020-12-21 20:54:03

Ministocin harkokin wajen Iran da kasashen Birtaniya, Rasha, China da kuma kasar Jamus, sun fitar da bayanin hadin gwiwa a yau Litinin da a ciki su ka jaddada cewa; Kudurin MDD mai lamba 2231 yana a matsayin ginshiki na raba duniya da makaman Nukiliya, kuma cigaba ne gagarumi a fagen diplomasiyya wanda zai bayar da gudunmawa wajen tabbatar da tsaro.
Ministocin
kasashen sun gudanar da taron ne ta hanyar bidiyo daga nesa a yau Litinin, a karkashin
jagroncin wakilin tarayyar turai Josep Borrell.
Wani sashe na sanarwar bayan taron ta kunshi cewa; Hukumar
makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA ) tana da muhimmanci a rawar da take
takawa waje aiwatar da manufar da kwamitin tsaro na MDD ya dora ma ta.
Don haka, ministocin sun amince da hukumar ta ci gaba da aiwatar
da nauyin da ya rataya a wuyanta.
Har ila yau, ministocin sun bayyana rashin jin dadinsu saboda
ficewar da Amurka ta yi daga cikin harjejeniyar.
013
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!