Kungiyar “ISWAP” Mai Dauke Da Makamai A Nigeria Ta Kashe Sojoji Da Kuma Garkuwa Da Wasu Fararen Hula

2020-12-21 20:50:34
Kungiyar “ISWAP”  Mai Dauke Da Makamai A Nigeria Ta Kashe  Sojoji Da Kuma Garkuwa Da Wasu Fararen Hula

Majiyar tsaro a Nigeria ta ce sojoji 5 ne su ka kwanta dama, sanadiyyar kwanton baunar da kungiyar Daular Musulunci A Yammacin Afirka ta yi musu a karshen mako.

Wannan harin dai ya zo ne sa’o’i, kadan da su ka gabata daga sace fararen hula 35 da aka yi a ranar juma’ar da ta gabata a garin Kuturu a kusa da jakana mai nisan kilo mita 25 daga birnin Maiduguri.

Ita dai kungiyar ISWAP, ta balle ne daga Boko Haram shekaru 6 da suka gabata.

A gefe daya gwamnan jihar ta Borno, Professor Babagana Umara Zulum ya ziyarci yankin Jakana da aka kai harin, inda ya nuna bacin ransa akan gajiyawar jami’an tsaro na tabbatar da tsaro a yankin.

Zulum ya kara da cewa; Abin takaici ne yadda a cikin shekaru biyu na bayan nan ake yawaita kai hari a wannan yankin da ke tsaianin Auno da Jakana, wanda wuce nisan kilo mita 20 ba.

Yankunan Arewa maso gabashin Nigeria da kuma Arewa maso yamma suna fama da matsalolin tsaro na masu tsaurin ra’ayin addini da kuma masu sace mutane domin karbar kudin fansa.

013Comments(0)
Success!
Error! Error occured!