Sojojin Kasar Yemen Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Saudiyya Maras Matuki

2020-12-21 20:44:56
  Sojojin Kasar Yemen Sun Harbo  Jirgin Leken Asirin Saudiyya Maras Matuki

Kakakin sojan kasar Yemen, Janar Yahya Sari’i ne ya sanar da cewa; Sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo jirgin sama maras matuki na Saudiyya samfurin CH4 ta hanyar amfani da makami mai linzami da ya dace a gundumar Ma’arib.

Sojojin Saudiyyar dai suna amfani da jirgin sama mara matuki samfurin CH-4 wajen kai hare-hare da makamai masu linzami daga nisan kilo mita 5000 daga sama.

Tun a shekarar 2015 ne dai Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen ta hanyar kafa kawancen da ya kunshi Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen Larabawan Afirka. Sai dai ya zuwa yanzu yakin nasu bai samar da nasarar da suke nema ba.

Adadin mutanen da su ka rasa rayukansu sanadiyyar yakin na Saudiyya ya haura dubu dari biyu, yayin da wasu dubun dubata su ka jikkata.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!