Iran, Ta Bukaci Wajabcin Aiki Da Tsarin Musaya Na INTEX

2020-12-21 14:39:11
Iran, Ta Bukaci Wajabcin Aiki Da Tsarin Musaya Na INTEX

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bukaci kasashen turai da su gaggauta inganta tsarin nan na musaya da ake kira INTEX, ta yadda ita ma zata mori tsarin a bangaren tattalin arziki.

A wata wasika da ya aike wa babban sakataren MDD, da shugaban kwamitin tsaron MDD, na wannan karo Iran za ta bukaci kasashen turan da suka cika alkawuran da suka dauka.

Wakilin Iran, a MDD, ya bayyana cewa matakin da Iran ta dauka na daina aiki da wasu bangarori da yarjejeniyar ta kunsa, ya biyo bayan da Amurka ta sabawa yarjejeniyar.

Game da tsarin musayar na bani-gishiri in baka manda (INTEX), M. Takht-Ravanchi, ya bukaci kasashen turai su nuna da gaske su ke a cikin shekaru biyu masu zuwa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!