Kasashen Gabashin Afrika Na Taro Kan Rikice-rikice A Yankin

2020-12-21 14:36:18
Kasashen Gabashin Afrika Na Taro Kan Rikice-rikice A Yankin

Kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin gabashin Afrika, na wani taron gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a yankin, duba da rikice rikice dake faruwa a wasu kasashen yankin.

Taron dake gudana a Djibouti, na duba halin da ake ciki game da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a kasashen Sudan ta kudu, da Sudan, sai kuma batun rikicin yankin Tigray na Habasha.

Wani batun kuma da taron ke tattaunawa shi ne takkadamar dake tsakanin kasashen Somaliya da Kenya, wanda har ya kai ga shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed, ya sanar da katse huldar diflomatsiya da Kenya, bisa zarginta da shishigi a harkokin cikin gidan kasar da kuma keta hurumin kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!