​Jalali: Harkokin Kasuwanci Da Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Iran Suna Tafiya Kamar Yadda Ya Kamata

2020-12-21 11:09:30
​Jalali: Harkokin Kasuwanci Da Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Iran Suna Tafiya Kamar Yadda Ya Kamata

Jakadan kasar Iran a kasar Rasha ya bayyana cewa, duk da takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran, harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakaninta da Rasha suna tafiya kamar yadda ya kamata.

A cikin wani wani bayani wanda ya wallafa a daren jiya, Jakadan kasar Iran a kasar Rasha Kazem Jalali, ya bayyana cewa takunkuman Amurka bas u iya hana gudanar da harkokin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Rasha da Iran ba.

Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, hulda tsakanin Rasha da Iran ba ta takaita ga bangarorin na harkokin kasuwanci da tattalin arziki ba kawai, alaka ce wadda ta hada bangarori daban-daban.

Dangane da batun ayyukan hadin gwiwa da ake gudanar a bangaren ayyukan danyen mai da dangoginsa tsakanin kasashen biyu, Jalali ya bayyana cewa, Rasha da Iran suna tattaunawa kan batun kasuwar mai, da kuma hanyoyin farfado da farashin mai a kasuwanninsa na duniya.

A jiya ne ministan main a kasar Iran Bijan Zangane ya kai wata ziyara a kasar China, inda ya tattauna da manyan jami’an gwamnatin kasar kan batutuwa da suka shafi harkar mai tsakanin Iran da China, inda a yau kuma zai isa birnin Moscow na kasar Rasha, domin ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha a kan wannan batu.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!