​Gwamnatin Pakistan Ta Karyata Bayanan Da Ke Cewa Tana Shirin Kulla Alaka Da 'Yan Sahyuniya

2020-12-21 10:50:16
​Gwamnatin Pakistan Ta Karyata Bayanan Da Ke Cewa Tana Shirin Kulla Alaka Da 'Yan Sahyuniya

Firayi ministan kasar Pakistan ya karyata rahotannin da ke cewa kasarsa tana shirin kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Shafin arab news ya bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da wata tashar talabijin ta kasar Pakistan, Firayi ministan kasar Imran Khan ya karyata rahotannin da ke cewa kasarsa tana gudanar da wata tattaunawa ta bayan fage, da nufin kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Firayi ministan na Pakistan ya ce, har kullum siyasar kasarsa ta ginu ne akan mara baya ga al’ummar Falastinu, kuma ba za ta taba ja baya dangane da haka ba, kuma kasar Pakistan ba za ta amince da Isra’ila a matsayin halastacciyar kasa da ta mamaye yankunan Falastinawa ba.

A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne kafofin yada labaran Isra’ila suka bayar da rahotannin cewa, gwamnatocin Amurka da Saudiyya na yin matsin lamba kan wasu kasashen musulmi da na larabawa kan su kulla hulda da Isra’ila, inda kuma a cewar rahoton wasu daga cikin kasashen sun amince da haka, da suka hada har da kasar Pakistan.

Kafin wannan lokain dai ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mahmud Quraishi ya kore wannan batu, inda ya jaddada cewa kasarsa ba za ta taba bin sahun masu kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!