Ole Gunner: Pogb Zai Bayar Da Mamaki A Manchsrer United Daga Nan zuwa Karshen Kakar wasanni

2020-12-21 10:34:27
Ole Gunner: Pogb Zai Bayar Da Mamaki A Manchsrer United Daga Nan zuwa Karshen Kakar wasanni

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa dan wasa Paul Pogba yana cikin farin ciki a kungiyar kuma zai bawa duniya mamaki daga yanzu har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

A kwanakin baya ne wakilin dan wasa Pogba kuma mai kula da harkokin wasanninsa, Mino Rioala ya bayyana cewa Pogba baya jin dadin wasa a Manchester United ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu

A watan Yunin shekara ta 2022 kwantaragin dan wasan tawagar Faransa zai kare, zai kuma iya barin Old Trafford a watan Janairun shekara ta 2022 a matakin wanda bai da yarjejeniya kuma Pogba mai shekara 27, ya buga wasanni goma a gasar Premier League har da shida da aka fara bugawa da shi a fili a kakar bana.

Sai dai tuni aka fara danganta dan wasan Faransa da kungiyoyi daban daban wadanda suka nemeshi a kwanakin baya kamar Real Madrid da Juventus da kuma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta kasar Faransa.

Sai dai kociyan kungiyar a wata hira da yayi da manema labarai ya tabbatar da cewa duk wanda yake kallon Pogba yasan yana cikin farin ciki a kungiyar kuma zai ci gaba da taimakawa kungiyar wajen samun nasara a wasanninsu na gaba.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!