Jami’an Tsaro Sun Ceto Wasu Daliban Makarantar Islamiyya 80 Da Yan Bindiga Suka yi Garkuwa Da su A Jihar Katsina

2020-12-20 20:43:25
Jami’an Tsaro Sun  Ceto Wasu Daliban Makarantar Islamiyya 80 Da Yan Bindiga Suka yi  Garkuwa Da su A Jihar Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa kwanaki biyu bayan ceto yan makarantar sakandiren gwamnatin ta kimiyya da ke garin Kankara daga hannun yan bingida, sai ga shi wasu yan bindigan a daren jiya sun sake sace wasu yan Makarantar Islamiya su 80 akan hanyarsu ta dawo wa daga wajen Mauludi da aka yi a Unguwar Alkasim da ke garin Dandume.

Yanzu haka dai jami’an yan sanda da hadin guiwar yan kato da gora sun samu nasarar ceto dukkan yaran da yan bindiga suka sace, gami da wasu mata 4 da shanu 12 da yan bindigan suka sato a kauyen Danbaure.

A nasa bangaren kakakin yan sanda Jihar ta Katsina ya fadi cewa: an samu asarar rayuka tare da jikkata da dama daga cikin barayin a lokacin artabun , tuni aka tura karin jami’an yan sanda domin kara tabbatar da tsaro da kuma tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu, sai dai a yace babu wanu jami’in yan sanda da ya rasu sakamakon lamarin.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!