Dan wasan kwallon Kafa Na Bercelona Lionel Messi Ya Kamo Pele Wajen Cin Kwallaye A Tarihi

2020-12-20 20:38:52
Dan wasan kwallon Kafa Na Bercelona Lionel Messi Ya Kamo  Pele Wajen Cin  Kwallaye A Tarihi

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan na kasar Agentina Lionel Messi mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Bercelona ya kamo shahararran dan kwallon kafar nan na Duniya dan kasar Brazil Pele kan tarihin da ya kafa na zura kwallaye 643 , kuma ya kamo shi ne bayan da ya ci wata kwallo a wasan da suka buga a jiya Asabar tsakaninsu da Valancia.

A gefe guda kuma za ku ji cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester city da Pairs St Germain sun bayyana aniyarsu ta dauko Lionel Messi din dan shekaru 33 da haihuwa sun ce suna da karfin guiwar cewa zai bar Barcelona nan ba da jimawa ba,

Shi kuwa dan wasan kwallon kafa na Liver pool dan kasar Masar mohammad salah mai shkaru 28 da haihuwa ya cewa alamuransa na hannun kungiyar da yake bugawa wasa, amma dai yana sha’awar kasancewa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ko kuma Barcelona.

An raba jadawalin gasar Supercopa inda za’a kara tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad da kuma Barcelona sai kuma Reaal Madrid da kuma Athletic a cikin watan janerun shekara ta 2021 mai kamawa.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!