Jami’an Tsaro Sun yi Arangama Da Dalibai Da ke Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta A Labanon

2020-12-20 20:31:34
Jami’an Tsaro Sun yi Arangama Da Dalibai Da ke Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta A Labanon

An yi Arangamar ne a bakin kofar shiga Jami’ar Amurka da ke unguwar Hamra a birnin Beirut na kasar ta Labanon.

Daliban sun fusata ne game da matakin da Hukumar jami’art ta AUB ta dauka na mayar da kudin makaranta gwagwardon yadda farashin dala yake akan Pound 3900 a daidai lokacin da farashin dala yake akan pound 1500 a kasar.

Wannan matakin zai sanya kudin makarantar ya yi tashin goron zabi da kashi 160 a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki da ba’a taba ganin irin ta ba a kasar, da kuma Dambarwar siyasa da ta cude a kasar.

Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu Zanga-zanar sa’ilin da suke kokarin kusantar babbar kofar shiga jami’ar. Sai dai daliban sun yi amfani da duwatsu da Bomb din kwalba akan jami’an yan sandan, da dama daga cikinsu sun jikkata sakamakon haka.

Masu Zanga- zangar suna ta rere taken yin tir da gwamnatin kasar kana sun yi kira gareta da a samar da ingantaccen Ilimin ga Alummar kasar.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!