​Zarif: Matukar Amurka Na A Cikin Gabas Ta Tsakiya Ba Za A Taba Samun Zaman Lafiya A Yankin Ba

2020-12-20 12:47:13
​Zarif: Matukar Amurka Na A Cikin Gabas Ta Tsakiya Ba Za A Taba Samun Zaman Lafiya A Yankin Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, matukar Amurka tana a cikin yankin gabas ta tsakiya, ba za a taba samun zaman lafiya a yankin ba.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana hakan ne a daren jiya a wata zantawa da ya yi da tashar Tulu News, inda ya jaddada wajabcin ficewar Amurka daga yankin baki daya, kafin samun nasarar duk wani shiri na zaman lafiya.

Ya ce dukkanin abubuwan da suke faruwa na a yankin abu ne sananne ne ga kowa, kan cewa Amurka da ‘yan korenta na yankin ne suke da hannu kai tsaye wajen haddasa su.

Zarif ya ce dole ne al’ummomin yankin su warware matsalolinsu a tsakaninsu, tare da yin aiki tare da juna domin ci gaban kasashensu, da kuma tabbatar da tsaro, wanda kasashen ketare ba za su iya tabbatar musu da shi ba.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya bayar da misalai kan irin rawar da Amurka ta taka wajen rusa kasashe irin su Afghanistan Syria Iraki da sauransu, tare da samar da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi domin bata sunan addinin muslucni da kuma rusa kasashen musulmi.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!