​Burtaniya: Musulmi Sun Bayar Da Gagarumar Gudunmawa Wajen Yaki da Corona

2020-12-20 12:43:43
​Burtaniya: Musulmi Sun Bayar Da Gagarumar Gudunmawa Wajen Yaki da Corona

Bayan bullar cutar corona a kasar Burtaniya, musulmin kasar ba zama ‘yan kallo ba kawai, sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen dakile cutar corona a kasar ta hanyoyi daban-daban.

Daga cikin matakan da musulmi suka dauka dai har da kula da masallatansu, tare da daukar matakai na tabbatar da cewa an kula da tsafta yadda ya kamata, da kuma kiyaye dukkanin ka’idoji na kiwon lafiya.

Malamai da limamai a masallatai da cibiyoyi na musulmi suna fadakarwa a kowane a cikin kasar Burtaniya, kan yadda ya kamata jama’a su rika kula da abubuwan da za su taimaka wajen dakile cutar, tare da bayyana hakan a matsayin daya daga cikin abubuwa na wajibia kan kowa.

Baya ga haka kuma, ana daukar matakai na saka magunguna a kowane lokaci a ikin masallatai da cibiyoyi na addinin musulunci a fadin kasar, wanda musulmin ne da kansu suke daukar nauyin yin hakan.

Haka nan kuma suna samar da watacen sanadarin kashe kwayoyin cuta da ake sanya wa a hannuwa, da kuma samar da takunkumin rufe baki da hanci, wanda dole ne duk wanda zai shiga masallaci ya yi amfani da su, da kuma kiyaye bayar da tazara.

A bangaren sauran ayyuka na kiwon lafiya da yaki da cutar corona a kasar Burtaniya kuwa, ana damawa da musulmi a dukkanin bangarori, kama daga bangaren likitoci, da kuma masu jinya da sauransu, babu wani fage wanda babu musulmi a cikinsa.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!