​An Gudanar Da Taron Girmama Qasem Sulaimai Da Muhandis A Majalisar Dokokin Iraki

2020-12-20 10:42:50
​An Gudanar Da Taron Girmama Qasem Sulaimai Da Muhandis A Majalisar Dokokin Iraki

Majalisar dokokin kasar Iraki ta gudanar da zaman taro na girmama manyan kwamandojin Hashd Al-sha’abi da Amurka ta yi wa kisan gilla.

Rahoton da tashar alalam ta bayar ya ce majalisar dokokin kasar Iraki ta gudanar da zaman taro na girmama manyan kwamandojin Hashd Al-sha’abi da Amurka ta yi wa kisan gilla kusan shekara guda da ta gabata a cikin birnin Bagadaza.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da shugaban majalisar dokokin Iraki Muhammad Halbusi, da ‘yan majalisa gami da wasu fitattun ‘yan siyasa da suka da Sayyid Ammar Hakim, da kuma wasu manyan jami’an tsaro.

A lokacin da yake gabatar da jwabinsa a wajen taron Faleh Fayyad shugaban rundunar Hashd Al-sha’abi ya bayyana cewa, kisan da Amurka ta yi wa Qasem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis da sauran dakarun da suke tare da su, babban laifi ne na kasa da kasa.

Ya ce ba zasu taba barin wannan lamari ya wuce haka nan ba tare da bin kadunsa da kuma daukar matakin da ya dace kan hakan ba, domin kuwa a cewarsa a yanzu haka ana bin kadun batun ta hanyoyi da suka da cewa da shar’a da kuma doka ta kasa da kasa.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!