AU Ta Kaddamar Da Shirin Kula Da Batutuwan Kaura A Nahiyar Afrika
2020-12-20 09:55:16

Tarayyar Afrika AU, ta kaddamar da wani shiri da zai rika tattarawa da nazarin bayanai dangane da kaura, wanda aka yi wa lakabi da African Migration Observatory.
AU ta ce gazawa da rashin bayanai kan kaura, sun hana mambobinta daukar dabarun da suka shafi batun.
Shirin, wanda aka kaddamar a Rabat na Morocco, zai saukaka aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasa ta Marrakesh kan batun kaura, ta hanyar tattara bayanai da inganta hadin gwiwa a nahiyar da kuma tsakanin kasa da kasa a fannin, tare da karfafa gudunmuwar kaura ga muradun ci gaba masu dorewa.
Shirin na AU, na da nufin magance bukatun nahiyar na ilmantarwa da kara fahimtar yanayin kaura.
Kwamishinar
AU mai kula da harkokin al’umma, Amira Elfadil, ta ce shirin shi ne irinsa na
farko a nahiyar, kuma ya alamta kokarin fara tattara sahihan bayanai dake da
nasaba da bukatun nahiyar a fannin kaura.
024
Tags:
tarayyar afrika au
bayanai dangane da kaura
a rabat na morocco
gudunmuwar kaura ga muradun ci gaba masu dorewa
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!