Nijar : Mutum 35,000 Ke Bukatar Tallafin Gaggawa A Yankin Tummour

2020-12-20 09:51:21
Nijar : Mutum 35,000 Ke Bukatar Tallafin Gaggawa A Yankin Tummour

A jamhuriyar Nijar, mutane kimanin 35,000 ne ke cikin bukatar gaggawa a yankin Toummour dake jihar Diffa a kudancin kasar mai fama da hare haren kungiyar boko haram.

A wata sanarwa da kwamitin kasa na kare hakkin bil adama ya fitar, bayan harin baya baya nan da kungiyar boko haram ta kai a cikin daren ranar 12 ga watan nan, kwamitin ya ce mutum 34 ne suka rasa rayukansu a harin na Toummour.

Daga cikn mutanen a cewar sanarwar ta CNDH, akwai mutum 10 da aka kashe ta harbin bindiga, hudu ta hanyar nutsewa a ruwa, sai kuma 20 wadanda gobara ta kashe sanadin wutar da aka bamkawa kauyen.

Ko baya ga hakan akwai daruruwan mutane da suka jikkata a harin, sai kuma hasarar dukiya iri daban daban da kuma dabbobi.

Tunda farko dai a wata sanarwa da hukumomin kasar suka fitar sun ce mutum 28 ne suka rasa rayukansu a harin na Toumour da kungiyar boko haram ta dauki alhakin kaiwa.

Tun bayan harin ne al’ummar yankin ke ci gaba da kauracewa gidajensu, lamarin da ya kara tsanantar halin da ake ciki a yankin da ya jima yana fama da matsalar tsaro data dagula al’amuran jin kai.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!