Afrika ta Tsakiya : Bozize Ya Musanta Shirya Juyin Mulki

2020-12-20 09:40:37
Afrika ta Tsakiya : Bozize Ya Musanta Shirya Juyin Mulki

Gwamnatin Bangui, a Afrika ta tsakiya, na zargin tsohon shugaban kasar da kokorin shirya juyin mulki, a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabenta.

A wata sanarwa data fitar gwamnatin Banguin, ta ce M. Bozize ya hada kai da gungun masu dauke da makamai domin kifar da mulki, a matsayin maida martani ga yin watsi da takararsa da kotun tsarin mulkin kasar ta yi a zaben shugabancin kasar.

Haka kuma gwamnatin na mai zargin gungun masu dauke da makamai da kai hare hare yanzu haka a yankunan arewa maso yammacin kasar.

Saidai tsohon shugaban kasar Francois Bozize, ya musanta zargin gwamnatin na shirya juyin mulki.

Al’amuran tsaro dai a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, na ci gaba da tabarbarewa a yayin da ya rage mako guda a je babban zaben kasar.

A ranar Laraba data gabata gungun masu dauke da makamai da dama a kasar sun gargadi shugaban kasar Faustin Archange Touadera, akan kada ya kuskura ya shirya zabubukan kasar.

Tuni dai MDD, ta sanar da aikewa da tawagar wanzar da zaman lafiya, wacce ke cikin shirin ko ta kwana bayan jerin hare haren da aka kaiwa wasu yankunan yammacin kasar ta Afrika ta tsakiya.

A ranar 27 ga watan nan ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa gami dana ‘yan majalisar dokoki a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!