MDD : Guteress Ya Yi Kira Ga Duniya Da Ta Ci Gaba Da Alakar Kasuwanci Da Iran

2020-12-19 20:21:29
MDD : Guteress Ya Yi Kira Ga Duniya Da Ta Ci Gaba Da Alakar Kasuwanci Da Iran

Babban Magatakardar MDD, Antonio Gutrres wanda yake gabatar da rahoto akan aiki da kudurin MDD mai lamba 2231 na yarjejeniyar Nukiliya ta Iran a 2015, ya bayyana cewa; Kudurin yana yin kira ne ga dukkanin kasashen duniya da su yi aiki da shi.

Antonio Guterres ya bayyana yarjejeniyar Nukilyar ta Iran da cewa tana tabbatar da cewa diplomasiyya da tattaunawa sun yi nasara wajen hana yaduwar makaman Nukiliya.

A wani sashe na rahoton babban magatakardar MDD, ya bayyana takaicinsa akan yadda Amurka ta janye daga yarjejeniyar ta Nukiliya, yana mai cewa; Sake dawo da takunkumin da kwamitin tsaron ya dauke, yana cin karo da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!