​Tsayin Dakan Alummar Iran zai sa Amurka ta Dawo Daga Rakiyar Sanya Mata Takunkumi

2020-12-19 14:58:38
​Tsayin Dakan Alummar Iran zai sa Amurka ta Dawo Daga Rakiyar Sanya Mata  Takunkumi

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya fadi a wajen wani taro da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta shirya cewa yayi Amanna tsayin Dakar da Alummar Iran ta nuna a tarihi zai sanya sabuwar gwamnatin Amurka ta canza tunaninta kan alummar kasar, kuma zai tilasta mata koma kan alkwuran da ta dauka karkashin yaryejejeniyar nulkiyar da aka cimma matsaya a kai a shekara ta 2015 kuma zai karya takunkumin da ta kakaba mata.

Gwamnatin Donald Trumph mai barin gado ta dawo da takunkumin da tsohon shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya daukewa Iran bisa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma tsakanin ta da sauran kasashe masu karfi na duniya. Kuma ya fice daga yarjejeniyar da aka cimma matsaya akai rana tsaka.

A nasa bangaren jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah sayyid Ali khamina’I ya bukaci kasar da kada ta bata lokaci koda sa’a daya ne kan batun cire takunkumin makutar hakan zai yi wu ta hanyar da ta dace da za ta bada tabbacin kare mutunci da martabar kasar

Wannan yana zuwa ne bayan da zababben shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyarsa na sake komawa kan yarjejeniyar nukiliyar iran da aka cimma matsaya akai.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!