Guterres Ya Yi Maraba Da Sakin Daliban Makarantar Kankara

2020-12-19 14:45:39
Guterres Ya Yi Maraba Da Sakin Daliban Makarantar Kankara

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da sakin yaran da aka sace a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da mataimakin kakakinsa, Farhan Haq ya fitar, Antonio Guterres ya yabawa matakin gaggawa da hukumomin Najeriya suka dauka wajen ceto yaran, yana mai kira da a gaggauta sakin wadanda suka rage, ba tare da wani sharadi ba.

Sakatare janar din ya kuma yi kira da a kara matsa kaimi wajen tsaron makarantu da sauran cibiyoyin ilimi a kasar, tare da nanata goyon baya da kudurin MDD na taimakawa gwamnati da al’ummar Najeriya a yakin da suke da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da manyan laifuffuka.

Shi ma asusun kula da kananan yara na majalisar wato UNICEF, ya yi maraba da sakin yaran da kungiyar BH ta yi ikirarin sacewa a arewa maso yammacin kasar cikin makon da ya gabata.

Wakilin asusun a Najeriya Peter Hawkins, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, hare-hare kan cibiyoyin ilimi abu ne da ya yi matukar keta hakkokin yara.

Rahotanni sun ce sama da yara ‘yan makaranta 300 ne aka sace a makon da ya gabata, bayan wani hari da aka kai makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Kankara a jihar Katsina.

Sojojin Najeriya sun ceto 344 daga cikinsu da yammacin ranar Alhamis.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!