​MDD ta yi Tir da kisan da sojojin Isra’ila suka yi wa wani yaro bapalasdine

2020-12-19 14:29:52
​MDD ta yi Tir da kisan da sojojin Isra’ila suka yi wa wani yaro bapalasdine

Kwararru kan kare hakkin bil Adama na Mdd sun bayyana kashe wani Yaro bafalasdine da sojojin HKI suka yi a matsayin kisan gilla kuma ya keta dokokin kasa da kasa,. kan sun bukaci da a gudanaar da bincike na musamman mai zaman kasan, game da kisan gillan da sojojin na HKI suka yi wata matashin bafalasdine mai suna Ali ayman dan shekaru 15 da haihuwa.

Shi dai wannan matashi an kama shi ne a farkon watan da muke ciki wajen zanga-zanga a gabar yammacin kogin jodan domin nuna rashin amincewa da zalunci HKI take yankin palasdinu ,kuma shi ne yaro na 6 da sojojin HKI suka kashe a wannan shekarar mai karewa ta 2020,

Maa’aikatar watsa labarai ta palasdinu ta zargi sojojin HKI da kashe yara matasa da gangan, ya kara da cewa kimanin matasa 3097 ne suka rasa rayuwakansu a hannun sojojin HKI daga lokacin da aka fara zanga zangar intifada a shekara ta 2000 zuwa yanzu.

Sai dai duk da tofin Allah tsine da kasashen duniya ke yi game da kashe yara da mata da sojojin HKI suke yi wannan bai hana gwamnatin Isra’ila ci gaba da yin kisan gilla kan yara kanana palasdinwa da take yi ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!