​Gharib Abadi: Babu Batun Tattaunawa Domin Cimma Wata Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya

2020-12-19 09:59:10
​Gharib Abadi: Babu Batun Tattaunawa Domin Cimma Wata Sabuwar Yarjejeniyar Nukiliya

Wakilin Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya jaddada cewa, babu batun wata tattaunawa domin cimma wata sabuwar yarjejeniya kan shirin Iran na nukliya.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria, wakilin Iran a hukumar makamashin nukiliya ta duniya Kazem Gharib Abadi ya bayyana cewa, babu gaskiya dangane da rahotannin da ke cewa, shugaban hukumar IAEA ya yi ikirarin cewa, dole ne a sake wata sabuwar yarjejeniya kan shirin Iran na nukiliya.

Gharib Abadi ya ce, babu gaskiya a wannan batu, domin hukumar IAEA ba ta da hurumin yin hakan, kuma ba za ta sanya kanta a cikin irin wadannan batutuwa na siyasa ba, domin kuwa aikinta ba na siyasa ba ne.

Ya ci gaba da cewa, babu batun sake wata tattaunawa domin cimma wata sabuwar yarjejeniya kan shirin Iran na nukiliya, domin kuwa an riga an cimma yarjejeniya tun fiye da shekaru 5 da suka gabata.

Ya ce abin da ake bukata wanda aka rasa shi ne yin aiki da ita kamar yadda aka rattaba hannu a kanta, kuma wannan shi ne abin da Iran take jira ta gani daga sauran kasashe bangarorin yarjejeniyar.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!