​Najeriya: Buhari Ya Bukaci Daliban Sakandaren Kankara Da Su Mayar Da Hankali Ga Karatunsu

2020-12-19 09:42:52
​Najeriya: Buhari Ya Bukaci Daliban Sakandaren Kankara Da Su Mayar Da Hankali Ga Karatunsu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci daliban sakandare na Kankara da aka karbo su daga hannun ‘yan bindiga, da su mayar da hankali ga karatunsu.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da wadannan dalibai a jiya a Katsina, bayan da gwamnatin Jihar Katsina ta karbe su daga hannun jihar Zamfara wadda ta karbo su daga hannun ‘yan bindigar.

A cikin jawabin da ya yi a lokacin da yake ganawa da daliban, wadanda akasarinsu kananan yara ne, shugaba Buhari ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda aka kubutar da su, ya kuma yaba wa gwamnatin jihar Katsina da jami’an tsaro, da kuma wadanda suka taimaka wajen kubutar da su.

Shi ma a nasa bangaren gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda aka kubutar da yaran ba tare da wani ya rasa ransa ba.

Sai dai a nasa bangaren gwamna jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa sun yi amfani da ‘yan bindigar da aka yi sulhu da su ne a jihar Zamfara wajen karbo yaran, kamar yadda kuma shugaban kungiyar Meyatti Allah ya taka muhimmiyar rawa cikin lamarin, daga karshe kuma gwamnatin jihar Zamfara tabi dukkanin matakan da suka dace har ta karbi yaran daga hannun ‘yan bindiga a daren Alhamis, kuma ta mika su ga gwamnatin jihar Katsina da jijjifin safiyar jiya Juma'a.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!