​FIFA: Lewandowski Ne Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya Na 2020

2020-12-19 09:00:10
​FIFA: Lewandowski Ne Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya Na 2020

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da tawagar kwallon kafar kasar Poland, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa mafi shahara a duniya na Fifa a shekarar nan ta 2020 mai karewa.

Dan wasan ya yi takara ne tare da dan kwallon tawagar Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi na Barcelona da tawagar Argentina wadanda a baya su ne suka mamaye gasar suke dauka a tsakaninsu.

Dan kasar Poland din, ya ci kwallaye 35 a wasanni 47 a bara da hakan ya taimaka wa Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar da ta wuce kuma Lewandowski, mai shekara 32, shi ne ya zama kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga da kofin kalubale na Jamus da na Champions League a bara.

Wannan ne karon farko da Lewandowski ya lashe kyautar da ya takara da dan kwallon Barcelona. Messi da na Juventus, Cristiano Ronaldo wadanda za’a iya cewa sun lashe kyautar a baya da yawa.

Sannan dan kasar Poland din ya dora a bana kan kwazon da ya yi a kakar da ta wuce, wanda ya ci kwallo 16 a wasanni 14 da ya yi wa Bayern Munich kuma masu koyar da tawagogin kwallon kafa da kyaftin-kyaftin na mambobin Fifa ne ke yin zaben da kuma ta yanar gizo da ‘yan jarida guda 200.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!