Najeriya : Daliban Kankara 520 Ke Hannun Boko Haram_Bidiyon Shekau

2020-12-17 21:53:42
Najeriya : Daliban Kankara 520 Ke Hannun Boko Haram_Bidiyon Shekau

Kungiyar boko haram, ta fitar da wani faifan bidiyo, da a cikinsa ta nuna wasu gomman dalibai data ce na makarantar kwalejin kwana ta maza ta Kankara ne data sace.

A cikin hoton bidiyon da aka saka na mintina shida da dakikoki 30 an nuno wani dalibi fuskarsa cike da kura yana cewa yana daga cikin dalibai 520 da mayakan Abubakar Shekau suka sace a ranar Juma’a data gabata a makarantar Kankara.

An kuma nuno sauran daliban a bayansa su ma fuskokinsu cike da kura, da alamu kuma suna cikin mayuyacin hali.

Baya ga hakan aka watsa wani sakon sauti na wani mutum da aka bayyana da Abubakar Shekau yana mai cewa ga mutane na, wannan kuma yaran ku ne.

Daliban sun Kara da cewa an kashe wasu daga cikinsu inda suka roki gwamnati ta biya bukatun kungiyar domin ta sake su.

Harin na makarantar Kankara dai ya maimaita abunda ya faru ga ‘yan matan makarantar sakandare ta garin Chibok a cikin shekara 2014, wanda kuma babban kalubale ne ga gwamnatin Shugaba Buhari, wanda ya cika shekaru 78 a wannan Alhamis.

Buhari, wanda dan asalin jihar Katsina ne dake shugabancin Najeriya, tun cikin shekra 2015, ya sanya yaki da kungiyar boko haram a cikin manyan alkawuransa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!