Faransa : Shugaba Macron Ya Kamu Da Cutar Korona

2020-12-17 21:48:06
Faransa : Shugaba Macron Ya Kamu Da Cutar Korona

Fadar shugaban kasa a Faransa, ta sanar da cewa shugaban kasar Emmanuel Macron, ya kamu da cutar korona.

A sanarwar da fadar ta Élysée, ta fitar ta ce gwajin da akayi wa shugaban kasar a ranar Alhamis, bayan ya soma jin wasu alamu ya nuna cewar ya harbu da cutar covid-19.

Sanarwar ta ce shugaba Macron, zai killace kansa na tsawon kwanaki bakwai, kamar yadda dokoki suka tanada, amma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga nesa ma’ana ta kafar bidiyo da kuma wayar tarho.

A halin da ake ciki dai tuni makusantansa da kuma wasu manyan jami’ai na kasar dama na ketare suka sanar da killace kansu, bayan yin mu’amulla da shi a baya bayan nan.

Daga cikinsu dai akwai firaministan faransar dana Spain da kuma na Portigal.

Saidai an ce gwajin da akayi wa matar shugaban na Faransa Brigitte Macron ya nuna cewa bata kamu da cutar ba.

Tuni dai wasu shugabbani da gwamnatin kasashen duniya suka fara isar wa da shugaba Macron sakon fatan samun sauki.

Kafin shugaba Macron dai akwai shugabannin da suka kamu da cutar korona, kamar takwaransa na Amurka Donald Trump, dana Barzil Jair Bolsonaro, sai kuma firaministan Biritaniya Boris Jonson, kuma duk sun warka daga cutar sun ci gaba da ayyukansu.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!