Nijar : Kotun Tsarin Mulki Ta Ja Kunnen ‘Yan Adawa

2020-12-17 21:44:20
Nijar : Kotun Tsarin Mulki Ta Ja Kunnen ‘Yan Adawa

Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar ta ce ba zata lamunta da take taken wasu jam’iyyun siyasar kasar ba, a daidai lokacin da ya rage kasa da kwana goma a je babban zaben kasar.

A sanarwar menema labarai data fitar kotun tsarin mulkin kasar, ta ce ba za ta amince ba da duk wata barazana ba ga mambobinta ko hukumar.

Duk wani wasa da kudurorinta ba abunda za’a lamunta da shi ne ba, wanda hakan sabawa dokoki ne.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu jam’iyyun adawa na kasar suka bukaci kotun data fayyace musu kace nacen da akeyi kan sahihancin takardun zama dan kasa na dan takarar jam’iyya mai mulki a kasar ta PNDS-tarayya cewa da Malam Bazoum Mohammed.

'Yan adawan dai na ci gaba da kalubalantar hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke in da ta wanke M. Bazoum din.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!