WHO : Masana Kimiyya Zasu Je China Domin Binciken Tushen Korona

2020-12-17 21:39:30
WHO : Masana Kimiyya Zasu Je China Domin Binciken Tushen Korona

Tawagar masana kimiyya ta kasa da kasa da hukumar lafiya ta duniya ta kafa domin binciko tushen kwayar annobar cutar korona za ta isa kasar China a watan Janairu na shekara mai shirin kamawa, kamar yadda wani kakakin hukumar ta WHO, ta sanar.

Jami’in dai bai yi bayyani ba sosai kan yadda tawagar za ta yi aikin, amma manyan jami’an hukumar ta WHO, da dama sun bukaci tawagar kwararunda ta isa yankin Wuhan na China, wanda ake kallon nan ne cutar t afara bulla.

Tawagar dai ta kunshi da masana kimiyya guda goma daga kasashen (Danmark, Biritaniya, Hollande, Austrea, Rasha, Vietnam, Jamus, da Amurka, da Qatar da kuma Japan).

Binciken dai zai maid ahankali ne kan tushen cutar da kuma yadda akayi ta yadu zuwa ga dan Adam.

Amurka wacce ita ce kasar da cutar ta fi wa illa, inda mutane sama da 300,000 suka mutu, na mai zargin mahukuntan Pekin, da kumbiya kumbiya kan batun cutar ta korona, sannan kuma hukumar lafiya ta duniya ta mika kai sosai ga kasar ta China.

Masana dai na ganin cewa jemage ne mai kwashe da kwayoyin cutar, saidai ba’a san dabba data yada ta ba zuwa dan adam.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!