EU, Ta Dakatar Da Baiwa Habasha Tallafi, Saboda Rikicin Tigray

2020-12-17 21:37:14
 EU, Ta Dakatar Da Baiwa Habasha Tallafi, Saboda Rikicin Tigray

Kungiyar tarayyar turai ta (EU), ta ce ta dakatar da tallafin kudi kimanin miliyan casa’in na Yuro, da ta ce zata baiwa kasar Habasha, saboda rikicin yankin Tigray.

EU, ta ce a halin da ake ciki yanzu ba zata iya zubawa kasar Habasha kudaden ba, wanda tallafi ne ga kasafin kudin da aka shirya zubawa a karshen wannan shekara, kamar yadda wata kakakin kwamitin kungiyar ta EU, dake Brussels, ta tabbatar da kamfanin dilancin labaren AFP.

Dole ne a cewar jami’ar, Pisonero-Hernandez, hukumomin Habasha, su bada cikakkiyar dama ta gudanar da ayyukan ceto ga mabukata a yankin na Tigray.

Kuma wasu daga cikin sharuddan da kungiyar ta EU, ta gindaya dole ne fararen hulasu samu mafaka a kasashe makobta, sannan kuma a kawo karshen kalamman nuna kiyaya da kabilanci .

Baya ga hakan kuma hukumomin kasar su gudanar da bincike kan zarge zargen take hakkin bil adama da kuma dawo da hanyoyin sadarwa da baiwa kafofin yada labarai damar shiga yankin na Tigray.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne, firaministan Habasha, Aby Ahmed, ya baiwa sojoji umarnin kaddamar da farmaki kan ‘yan kungiyar (TPLF), dake rike da iko a yankin na Tigray, wanda kuma a baya baya nan suka fara bijirewa gwamnatin tarrayya.

Rikicin na yankin Tigray, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, a cewar kungiyar International Crisis Group, dake bibiyar rikice rikice a duniya, sai kuma mutum 50, 000 da rikicin ya tilastawa tserewa daga gidajensu a cewar MDD.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!