Iran Ta Kira Yi Amurka Da Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Syria

2020-12-17 13:58:35
Iran Ta Kira Yi Amurka Da Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Syria

Jakadan Iran a MDD Majid Takht-Ravanchi wanda ya yi bayani yadda kasarta ta taimakawa gwmanati da al’ummar Syria wajen fada da ayyukan ta’adanci, ya yi kira ga Amurka da ta janye sojojin da ta girke a kasar.

Takht-Ravanchi, wanda ya ke gabatar da jawabi a wurin taron da kwamitin tsaron MDD ya shirya dangane da; Halin da Syria take ciki ta fuskokin tsaro da yanayin rayuwar al’ummar kasar, ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga dukkanin duniya da ta girmama hurumin kasar Syria da cin gashin kanta da ‘yancinta na siyasa.

Har ila yau jakadan na Iran a MDD ya ce; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana cikin shirin bayar da gudunmawa domin samo mafita akan rikicin kasar Syria.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!