An Yi Gargadi Akan Dawowar Harkar Fasa Kwauri Bayan Bude Wasu Iyakokin Nigeria

2020-12-17 13:54:04
 An Yi Gargadi Akan Dawowar Harkar Fasa Kwauri Bayan Bude  Wasu Iyakokin  Nigeria

A jiya Laraba ne Shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya sanar da sake bude wasu iyakokin kasa guda hudu nan take.

Ministar kudu da tsare-tsaren ayyukan kasa Zainab Ahmed ce ta fadawa manema labaru hakan a karshen taron da majalisar zartarwa ta yi, sai dai ta jaddada cewa; babu wani sauyi a haramcin da aka yi wa shinkafa da kaji da dangoginta.

A gefe daya kwararru a harkar kasuwanci da su ka hada cibiyar kasuwanci ta jihar Lagos, da kungiyar masu noman kaji da cibiyar Bakunan Nigeria, sun yi kira ga gwamnati da ta tsananta sanya idanu akan iyakokin domin hana hana fasa kwauri.

Acikin watan Ogusta na 2019 ne da gwamnatin tarayyar kasar ta rufe iyakokin kasa domin dakile harkar fasa kwauri.

Iyakokin da aka sanar da budewa a jiya sun hada Seme, da ke kudu maso yamma, sai Illa a Arewa masu yamma, da Mfun da ke kudu masu kudu, sannan kuma Maigatari da ke Arewa maso yamma.

Ministar kudin ta Nigeria ta kuma ce za a bude sauran iyakokin kafin ranar 31 ga watan Disamba na wannan shekara ta 2020 da ake ciki.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!