Noman Mangwaro Ya Yankewa Mutanen Wani Kauye Talauci A Kasar Sin

A shdekarar 2019 da ta gabata, mazauna garin sun sami damar shuka mangwaro a cikin eka 10,000 da hakan ya sa kudaden shigarsu ya karu da dalar Amurka 2,444,8.
Shugaban hukumar fada da
talauci a a kauyen Longjing Liang Jie ya bayyana
cewa; A tashin farko mutanen garin ba su da masaniya akan yadda ake shuka
mangwaro, kuma da ace sun dogara ne da hanyar gargajiya ta yin shuke-shuke to
da ba su moriyar mangwaron da su ka shuka ba.
Shugaban jam’iyyar gurguzu a
kauyen, Li Xiangyang ya ce; Bayan da aka yi namijin kokari na inganta mangwaron
da ake nomawa, an sami rubanya yawan mangwaron da ake nomawa a cikin kauyen.Da
aka shiga cikin watan Oktoba na wannan shekara ta 2020 da ake ciki kuwa, babu
wani talaka da ya saura a cikin kauyen na Longjing.
Da dama daga
cikin iyalai a kauyen sun samu ci gaba
ta fuskar tattalin arziki, bayan da su ka shiga cikin tsarin na noma mangwaro.
Li Yuangui wanda a shekarar 2014 yana ciki wadanda aka rubuta sunayensu a cikin
talakawa,yanzu ya sami sauyin yanaki saboda rungumar noman na mangwaro.
013