Shugaban Kasar Turkiya Ya Bayyana Takunkumin Amurka Akan Kasarsa Da Cewa; Keta Hurumin Turkiya Ne

2020-12-17 13:41:20
 Shugaban Kasar Turkiya Ya Bayyana Takunkumin Amurka Akan Kasarsa Da Cewa; Keta Hurumin Turkiya Ne

Shugaban na kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya fada a jiya Laraba cewa; Wannan wane kawance ne tsakaninmu ? Wannan matakin yana nufin keta hurumin kasarmu ne.”

Shugaban na Turkiya yana nuni ne da kawancen da yake a tsakanin kasarsa da Amurka a karakashin Yarjejeniyar kawancen tsaro ta “Nato”.

Amurka ta kakaba wa kasar Turkiya ne takunkumi saboda sayen makaman tsaron kai daga hare-hare daga sama wanda kirar kasar Rasha ne.

Har ila yau takunkumin na Amurka ya shafi cibiyar da ta kunshi kamfanonin tsaro na kasar ta Turkiya, da kuma shugabanta Isma’il Dimir da kuma wasu jami’an da suke karkashinsa.

Shugaba Rajab Tayyib Urdugan ya kara da cewa; Tuni Turkiya ta waje wannan matakin na takunkumi zai kawo mata cikas a ci gaban da take yi.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!