Daukar Fansar Kisan Da Aka yi Wa Janar Kasim Sulemani Ba Makawa Kuma Za’a yi Shi A Lokacin Da Ya Dace

2020-12-17 10:26:20
Daukar Fansar Kisan Da Aka yi Wa Janar Kasim Sulemani Ba Makawa Kuma Za’a yi Shi A Lokacin Da Ya Dace

Jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatullah Sayyed Ali Khamina’i ya bayyana a lokacin wata ganawa da kwamitin shirya taron cika shekara guda da shahadar babban kwamandan yaki da ta’adanci na Iran Janaral Kasim Sulaimani da kuma Abu Mahadi Al-muhandis cewa daukar fansa kisan gillan da kasar Amurka ta yi wa Kasim Sulemani lamarin ne da babu makawa kuma za’a aiwatar da shi a duk lokacin da ya dace.

Dukkan wadandan kwamandojin guda biyu sun yi shahada ne a wani hari da aka kai musu da jirgi mara matuki bisa umurnin shugaban kasar Amurka mai barin gado Donald Trumph a kusa da filin saukar jiragen sama na birnin Bagadaza na kasar Iraki a ranar 3 ga watan Janerun shekara da muke ciki, wanda Janar Sulemani ya je ziyarar aiki ne bisa gayyatar da gwamnatin kasar Iraki ta yi masa.

Har ila yau jagoran ya kara da cewa Jana’izar da ka yi musu da ta samu halartar miliyoyin mutane lamari ne da ba za’a taba mantawa da shi ba kuma ya jefa ma’abota girman kai na duniya cikin mamaki , kuma shi ne mari na farko a fuskar Amurka.

Kuma kai hari kan sansanin sojin Amurka a Ainul Asad dake Iraki shi ma wani mari ne a fuskar Amurka , sai dai wannan ya banbanta da martani mai tsananin da zaa’a kai da yake jiran wadanda ke da hannu wajen kashe Kasim Sulemani.

Daga karshe jagoran ya nuna cewa shahadar Kasim Suleman mai cike da tarihi ta mayar da shi wani babban gwarzo ba kwai a kasar Iran ba, hatta a wajen dukkan al’ummar musulmi.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!