Kungiyar Kare Hakkin Dan Adama Ta “Amnesty International” Ta ce Harkar Ilmi A Arewacin Nigeria Na fuskantar Babbar Barazana
2020-12-17 10:19:27

A cikin wani bayani da Daraktan kungiyar ‘Amnesty International’ a Najeriya, Osai Ojigho ya fitar ya bayyana cewa: matsalar tsaron da Arewacin Nigeria ke ciki ta sanya harkar ilmi a yankin cikin mawuyacin halin na rashin tabbas.
Har ila yau
Kungiyar ta kara da cewa : Sace dalibai 333 a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta
garin Kankara a Jihar Katsina, babbar barazana ce ga harkar ilimin zamani a
arewacin kasar don haka ya zama wajibi a samar da tsaro ga dukkan makarantu domin kare rayukan daliban.
Ranar Talata
da ta gabata ne aka nuno shugaban kungiyar boko haram a wani faifan bidiyo yana
fadin cewa: “ Mu ne muka kama daliban
makarantar domin mu daukaka addinin Musulunci,
Mun yi haka ne domin mu hana yara karantun boko. Saboda Allah da Annabinsa ba su halasta wa musulmi yin karatun boko ba.”a
riyawarsa.
Daga karshe kungiyar ta “Amnesty international” ta yi kiran da a gaggauta ceto yaran Makarantar da aka yi garkuwa da su kana ta nuna takaicinta game da kashe daruruwan malaman makaranta da aka yi daga farkon yakin Boko Haram zuwa yanzu.
Tags:
kungiyar kare hakkin dan adama ta “amnesty interna
osai ojigho
sace dalibai 333 a makarantar sakandaren
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!