Mayakan Kungiyar Taliban Sun Kashe Wasu Yan Sanda 13 A Hari Da Suka Kai a Wurin Binciken Ababen Hawa A Kasar Afghanistan

2020-12-17 10:12:33
Mayakan Kungiyar Taliban Sun Kashe Wasu Yan Sanda  13 A Hari Da Suka Kai a Wurin Binciken Ababen Hawa A Kasar Afghanistan

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mayakan kungiyar Taliban sun kai hari kan wajen binciken ababen hawa a kusa da gadar Khumri a babban birnin lardin Baglan ta Arewa inda ya yi sanadiyar mutuwar yan sansa 13 tare da jikkata wasu da dama. Tuni an kwashe wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Aunuddin sayad domin yi musu magani.

Mai magana da yawun jami’an yan sanda na yankin Ahmad Javad ya tabbatar da kai harin, kuma tuni kungiyar Taliban ta sanar da alhakin kai harin.

A wani bangaren kuma wasu jami’an tsaro 5 da wasu mayakan Taliban 17 sun mutu bayan da dakarun tsaron gwamnatin kasar ta Afghanistan suka kai hari a kudancin lardin Uruzgan.

Tashe -tashen hankula sun kara kamari a sassa daban –daban na kasar ta Afghanistan duk da tattaunawa da ake yi tsakanin gwamnati da kungiyar Taliban da zimmar kawo karshen yaki da yaki ci yaki cinyewa a kasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!