Dan Wasan Kwallon Kafa Na Juventus Cristiano Ronaldo ya zubar da Fenariti A Wasan Da Suka yi Da Atalanta

2020-12-17 10:08:48
Dan Wasan Kwallon Kafa Na Juventus  Cristiano Ronaldo ya zubar da Fenariti A Wasan Da Suka yi Da Atalanta

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta tashi wasa 1-1 da Atalanta a gasar cin kofin Serie A da suka kara a jiya Laraba, Wannan dai shi ne wasa na shida da mai rike da kofi Juventus ta yi canjaras a bana, bayan buga wasa a mako na 12 a gasar.

Federico Chiesa shi ne ya fara ci wa Juventus kwallo mai kayatarwa daga wajen da'ira, . Atalanta ta farke kwallo ta hannun Remo da hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.

Cristiano Ronaldo ya buga fenariti, amma mai tsaron raga Gollini ya tare kwallon. Ronaldo ya samu damar kara na biyu, amma dai kwallon ba ta shiga ragar Atalanta ba.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lallasa takwararta ta Real Sociedad da ci 2-1 a wasan da suka buga a jiya laraba a , yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ita ce ke da maki 26 a saman tebur, sai kuma Real Sociedad ke bi mata ita ma da maki 26 Ita kuwa Barcelona ita ce ta 5 da maki 22.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!