​Majalisar Wakilan Najeriya Tana Matsa Lamba Kan Gwamnati Domin Kubutar Da Dalibai Daga ‘Yan Bindiga

2020-12-16 19:11:39
​Majalisar Wakilan Najeriya Tana Matsa Lamba Kan Gwamnati Domin Kubutar Da Dalibai Daga ‘Yan Bindiga

Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar da ta kara zage dantse wajen tabbatar da cewa dukkanin daliban da aka yi garkuwa da su, sun dawo da ransu da lafiyarsu ga iyayensu, da hakan ya hada da daliban makarantar Chibok da kuma daliban baya-bayan nan da aka yi garkuwa da su a Kankara da ke jihar Katsina.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta aiwatar da ayyuka kariya ga dalibai da malamai domin tabbatar da kare dalibai da malamansu daga hare-haren ‘yan bindiga, domin baiwa sashin ilimi damar ci gaba da tafiya ba tare da wata barazana ba.

Sannan kuma sun nemi gwamantin da ta gabatar da shirin kariyar makarantu a gaban majalisar kasa, domin amincewa da wannan shiri, ta yadda shirin zai fara gudana ba tare da wani bata lokaci ba.

Haka nan kuma ‘yan majalisar wakilan sun bukaci gwamnatin da ta sake nazarin matakan tsaronta domin kuwa a cewarsu sashin na bukatar garanbawul.

Dukkanin wadannan shawarwarin suna zuwa ne bayan da aka gabatar da wani kudurin da ke kiran a gaggauta ceto makarantu, bayar da kariya ga makarantu da cibiyoyin ilimi, dakile aikace-aikacen ‘yan bindiga, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!