MDD: Dole Ne Sojojin Haya Su Fice Daga Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci
gaggauta ficewar Sojojin haya da na kasashen ketare daga Libya, wadanda
Majalisar ke zargi da rura wutar rikicin kasar.
Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin
Duniyar yayin wani zaman sirri daya gudanar ta bidiyon Internet, ilahirin
mambobinsa 15 sun amince da kudirin tilastawa sojojin ketaren su gaggauta
ficewa daga kasar wadda ke ci gaba da fuskantar rikici tun bayan hambarar da
gwamnatin marigayi Kanar Gaddafi a shekarar 2011, da ‘yan tawayen kasar suka yi
tare da taimakon kasashen turai,
musamman Faransa, Burtaniya, Italiya da kuma Amurka.
Kwamitin ya ce bisa tanadin
yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarori masu rikici da juna suka cimmawa a
ranar 23 ga watan Oktoba, babu bukatar sojin haya ko na ketare a cikin kasar.
Gwamnatin kasar Turkiya ta jibge
dubban sojoji gami da mayakan da suke yi mata biyya a Syria, wadanda mafi
yawansu ‘yan kasashe ne daban-daban da ke cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar
jihadi, wadanda aka kwaso su zuwa Syria, yayin da kuma a yanzu aka kwaso wasu dubbai daga cikinsu
zuwa Libya, kamar yadda rahotannin majalisar dinkin duniya gami da na
kungiyoyin farar hula na kasa da kasa suka tabbatar da hakan.