Ana Ci Gaba Da Rufe Makarantun Sakandire A Arewacin Nigeria

2020-12-16 08:59:15
  Ana Ci Gaba Da Rufe Makarantun Sakandire A Arewacin Nigeria

Tun bayan sace dalibai daga makarantar kwana ta karamar hukumar kankara da aka yi a jihar katsina, da kuma rufe dukkanin makarantun jihohin da gwamnati ta yi, wasu jihohin arewacin kasar suna ci gaba da bin sahu.

A jiya Talata jihohin Jigawa, kano da Kaduna sun sanar da rufe makarantun na sakandire sai sai illa masha Allahu.

A jihar kano, gwamna Abdullahi Ganduje ta bakin kwamishinan lafiya Muhammad Kiru ne ya sanar da rufe makarantun nan take tare da umartar iyayen yara da su dauke ‘ya’yansu.

A can jihar Zamfara kuwa, gwamnati ta sanar da rufe makarantu 10 ne saboda barazanar da suke fuskanta daga masu dauke da makamai.

A jihar Kaduna kuwa an

sanar da rufe makarantun ne bisa dalili na dawowar cutar corona a zahiri.

013
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!