Amurka Ta Kakaba Wa Kungiyar “Sarayal-Mukhtar” Ta Kasar Bahrain Takunkumi

2020-12-16 08:54:07
Amurka Ta Kakaba Wa Kungiyar “Sarayal-Mukhtar”   Ta Kasar Bahrain Takunkumi

Amurka Ta Kakaba Wa Kungiyar “Sarayal-Mukhtar” Ta Kasar Bahrain Takunkumi

Tashar talabijin din ‘almayadeen’ ta bayar da labarin da yake cewa; Baitul-malin kasar Amurka ya sanar da takunkumi akan kungiyar ‘Sarayal-Mukhtar” ta kasar Bahrain.

Rahoton Baitul-malin kasar Amurkan ya bayyana kungiyar a matsayin barazanar tsaron kasar, tare da bayyana matakin da cewa sako ne mai karfi zuwa ga Iran.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pempeo ya riya cewa kasar tasa ba za ta bari kungiyoyi masu alaka da Iran su ci gaba da zama barazana ga Amurkan ba.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!