Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Nada Wani Sabon Manzo Zuwa Kasar Libya

2020-12-16 08:51:05
 Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Nada Wani Sabon Manzo Zuwa Kasar Libya

Kwamitin tsaron ya nada Nickolai Mladenov a matsayin manzo zuwa kasar Libya,domin maye gurbin Ghassan Salama da ya sauka daga kan mukamin nasa a cikin watan Maris, saboda sukewa da ya yi da aikin.

A cikin watannin bayan nan dai an sami ci gaba na azo a gani ta fuskar zaman lafiya da sulhu a tsakanin bangarorin da suke fada da juna a kasar ta Libya.

Kasashen Moroko da Tunisiya sun taka rawa wajen karbar bakuncin zaman tattaunawa a tsakanin banagrorin gwamnatocin Libya da suke da matsugunai da Tripoli da kuma Tubruk.

Kasashen larabawa sun rabu gida biyu a tsakanin masu goyon bayan janar Halifa Hfatar da yake iko da gabashin kasar, da kuma gwamnatin al-Siraj mai matsuguni a Tripoli.’

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!