Za A Sake Bude Filayen Jiragen Sama Na Kasa Da Kasa Biyu A Syria

2020-12-16 08:47:55
Za A Sake Bude Filayen Jiragen Sama Na  Kasa Da Kasa Biyu A Syria

Majalisar Ministocin kasar Syria ta amince da a sakebude filayen saukar jiragen sama na kasa da kasa da na Laziqiyya a ranar Litinin mai zuwa.

Har ila yau majalisar ministocin ta kuma sanar da cewa za a yi wa wani filin saukar jiragen saman na kasa da kasa da ke Qamishli gyara domin a sake bunkasa shi a nan gaba.

FIlin saukar jiragen sama na Halab shi ne na biyu a kasar bayan na babban birnin kasar Damascuss., kuma yana a matsayin daya daga cikin muhimman cibiyoyin kamfanin jiragen sama na kasar ta Syria.

Kasar Syria dai ta yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda tun daga 2011 wanda ya yi sanadiyyar lalacewar muhimman cibiyoyin kasar, baya ga asarar rayuka.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!