Najeriya : Ana Ci Gaba Da Nuna Takaicin Sace Daliban Kankara

2020-12-15 22:16:57
Najeriya : Ana Ci Gaba Da Nuna Takaicin Sace Daliban Kankara

A Najeriya, bangarori daban daban na al’ummar kasar na ci gaba da nuna takaici game da sace daruruwan dalibai makarantar sakandaren kwana ta Kankara dake jihar Katsina a arewa maso yammacin kasar.

Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya wato CNG, ta sha alwashin fara zaman dirshen a garin Daura da ke jihar Katsina don nunawa shugaban kasar Muhammadu Buhari damuwarsu kan abun da ya faru na sace daliban na Kankara.

Kafin dai Jama’a da dama dai na ganin cewa gwamnatin kasar bata dauki darasi ba, duba da abunda ya faru ga dalibai mata a makarantar sakandaren Chibok dake jihar Borno a cikin shekara 2014.

A halin da ake ciki dai kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin sace daliban na makarantar sakandaren kwana ta Kankara.

Shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ne yayi ikirarin sace daliban cikin wani sakon murya da ya fitar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!