Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Amurka Kan Turkiyya

2020-12-15 22:12:23
Iran Ta Yi Tir Da Takunkumin Amurka Kan Turkiyya

Iran, ta yi allawadai da takunkumun da Amurka ta kakaba wa Turkiyya.

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, ya bayyana a shafinsa na twitter, cewa amfani da takunkumin da Amurke ke yi kan kasashe ya wuce gona da iri.

M. Zarif, ya ce sabbin takunkuman kan Turkiyya, abun takaici ne, muna goyan bayan al’ummar kasar ta Turkiyya da gwamnatinta.

A jiya ne dai gwmanatin Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan kasar ta Turkiyya, saboda sayan makaman garkuwa samfarin S-400 kirar kasar Rasha.

Ita ma dai a nata bangare kasar ta Rasha, ta yi tir da takunkumin Amurkar kan kasar ta Turkiyya.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!